Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana ranar Juma’a 26 ga watan Agusta, amatsayin ranar hutu domin murnar cikar jihar shekara 31 da kafuwar.
Hakan na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Hussaini Ali Kila.
Da yake ayyana hutun amadadin gwamna Muhammad Badaru Abubakar, shugaban ma’aikatan ya taya ma’aikatan gwamnati da daukacin al’ummar jihar Jigawa murnar zagayowar wannan rana.
Sanarwar da mai magana da yawun offishin shugaban ma'aikata da sakataren gwamnati a Jigawa Sama'ila Dutse ya fitar, gwamnan ya bukaci al'ummar Jihar suyi amfani da ranar waje yin addu'a ga Jigawa da kasa baki daya.
Ta kara da cewa, “a bisa ga haka, akwai kyakkyawan fata cewa dukkan ma’aikatan gwamnati da daukacin al’ummar jihar za su yi amfani da hutun nan kwana daya wajen gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya samar da yanayi mai kyau da zaman lafiya sannan su yi addu’ar Allah ya kawo dauki aka matsalolin tsaro da ke addabar kasarnan.
Idan za a iya tunawa, an kafa jihar Jigawa ne daga tsohuwar jihar Kano a wata ranar Talata 27 ga watan Agusta na shekarar alif 1991 lokacin shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
..