Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce jam’iyyar APC ba ta da dan takarar Sanata a mazabar Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.
Idan za’a iya tunawa dai Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan mai wakiltar Yobe ta Arewa da kuma tsohon Gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma na fafutukar neman tikitin takarar sanata a jam’iyyar APC bayan sun sha kaye a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
Sai dai kwamishinan INEC na kasa, Festus Okoye ya ce hukumar zabe ba ta amince da duk wani dan takarar jam’iyyar APC na shiyyar sanatocin biyu ba.
Ya ce an tura sunaye guda biyu daga mazabun biyu kuma hukumar ta ki wallafa sunayensu saboda ba mutanen da suka fito daga sahihin zaben fidda gwani na jam’iyyar ta gudanar ba ne bisa sanya idanu na hukumar INEC.