Gwamnatin Taraiyya ta baiyana cewa babu wata tartibiyar yarjejeniya da suka kulla tsakaninsu da kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, Wadda a yanzu take dakon saka sa hannun shugaban kasa.
Ministan kwadago da samar da Guraban aiki, Sanata Chiris Ngige ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun Mataimakin Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na ma’aikatar, Mister Oladije Oshundun, wadda aka fitar jiya a Abuja.
Ministan Ngige ya baiyana cewa karin hasken ya zama wajibi, la’akari da wasu bayanai da Shugaban Kungiyar ASUU Farfesa Emmanuel Osodoke ke yiwa yan Najeriya da kuma sauran shugabannin rassan kungiyar, inda yake yin kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saka hannu kan yarjejeniyar da yayi ikirarin sun kulla tsakaninsu da gwamnati.
A cewar ministan kwadagon, Babu wata tartibiyar yarjejeniya da aka kulla tsakanin kungiyar Malaman Jami’oin ta kasa da kuma gwamnati.