On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Babu Wani Umarni Da Muka Samu Kan Shirin Fara Afkawa Sojojin Juyin Mulkin Nijar - Rundunar Sojojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce har yanzu ba ta samu wani umarni ba na fara daukar matakin soji, kan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya bayyana haka a yau a lokacin da yake mayar da martani ga wani rahoton yanar gizo dake cewa rundunar na shirya dakarunta domin daukar matakin soji a Jamhuriyar Nijar.

Janar Gusau yace matakin amfani da karfin sojoji shine mataki na karshe da ya kamata a dauka kan al’amarin idan duk wani zabi ya gaza a tattaunawa da masu yunkurin juyin mulki da kuma mayar da gwamnatin Jamhuriyar Nijar kan tsarin mulki.

Ya yi nuni da cewa, rundunar sojin Najeriya ba za ta iya ci gaba da yin shiri da  kowace kasa ta ECOWAS ba, ba tare da izini daga hukumomin shugabannin kasashe da gwamnatoci ba.