On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Babu Wani Umarni Da Kotu Ta Bayar Na Binciken Lafiyar Gwamna Akeredolu - Gwamnatin Jihar Ondo

Gwamnatin jihar Ondo ta yi watsi da rahotannin baya-bayan nan da ke nuni da cewa akwai wani umarnin kotu da ya umarci majalisar dokokin da kakakinta Olamide Oladiji da su kafa kwamitin lafiya domin tantance lafiyar Gwamna Rotimi Akeredolu.

Gwamnatin ta bayyana rahoton amatsayin na bogi, inda ta ce abunda ake yadawa bai yi daidai da shari'ar da kotuna ke ci gaba da yi akan al’amarin ba.

A wata sanarwa da babban mai shari’a na Ondo, Charles Titiloye ya fitar, ya ce kotun ta bayar da wani izini ne kawai ga lauyoyi da  kuma bangarorin shari’ar.

Titiloye ya ce ba a baiwa gwamnatin jihar Ondo bayanai kan zaman  kotu ba ko kuma ta samu damar gabatar da nata bangaren ba kan al’amarin.