On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Babu Wani Koma Baya Kan Rashin Amincewa Da Bukatarmu A Gaban Kotu - Jam'iyyar PDP

Jam’iyyar PDP ta ce kin amincewa da bukatar da ta yi na nuna yadda ake shari’ar karrakin zaben shugaban kasa kai tsaye ba wani koma-baya ba ne.

Idan za’a iya tunawa a jiya ne kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta ki amincewa da bukatar dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar daken a rika nuna zaman kotun kai tsaye.

Da yake magana da manema labarai bayan kotun ta yanke hukuncin, lauyan PDP, Eyitayo Jegede ya ce maimakon su tsaya kan kin amincewa, jam’iyyar da dan takararta a shirye suke don kan rahoton share faga gabanin sauraron karar.

Dangane da hade dukkan koke-koke na kalubalantar zaben Bola Tinubu, Jegede ya ce dokar kasa ce ta tilasta batun, don haka ba su da wata adawa a kai.