Gwamnatin Jihar Kano ta ce babu wata kwakkwarar hujja da aka samu daga takardun karar ‘yan sanda da ke tuhumar shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa da laifin kisan kai kan rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane a mazabar sa a zaben 2023. Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Musa Abdullahi Lawan, shine ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau, inda ya kara da cewa an samu kura-kurai sosai bayanan shaidun gani da ido. Lawal ya ce gwamnatin jihar na da isassun hujjoji da ke nuna cewa magoya bayan NNPP ciki har da wadanda
Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Musa Abdullahi Lawan, shine ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau, inda ya kara da cewa an samu kura-kurai sosai bayanan shaidun gani da ido.
Lawal ya ce gwamnatin jihar na da isassun hujjoji da ke nuna cewa magoya bayan NNPP ciki har da wadanda suka mutu sune ake zargin sun kunna wuta da gangan k
akan titi domin hana fita da sakamakon zaben zuwa INEC kafin wutar ta bazu zuwa ofishin jam’iyyar.
A cewarsa, ba a ga harsashi a wurin da aka aikata laifin ba, haka kuma ba a cire harsashi daga wadanda suka jikkata da ake zargin an harbe su.
Ya kara da cewa babu wani cikakken bayani akan mamatan da jam’iyyar NNPP ta yi ikirarin cewa sun mutu a wani asibiti mai zaman kansa kuma ba a gudanar da bincike akan sauran gawarwaki guda biyu ba kafin a binne su domin a tabbatar da musabbabin mutuwarsu.