Karamin ministan kwadago mai barin gado, Festus Keyamo, yace nadin karamin minister da shugaban kasa keyi baya kan doron kundin tsarin mulki.
Keyamo wanda ya bayyana hakan a jawabansa na taron majalissar zartaswa na bankwana a Abuja, yace babu wani tanadi na nadin karamin minista a kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yiwa gyaran fuska.
Ya godewa shugaba Buhari kan damar da ya samu ta hanyar nadin da aka yi masa, amma ya lura cewa wasu ministocin sun yi ta gunaguni sannan sun kasa jajircewa su fadin albarkacin bakinsu.
Itama karamar ministar babban birnin tarayya, Hajia Ramatu TijaniAliyu ta yi kira da a soke mukamin karamin minister.
Karamar Ministar babban birnin tarayya ta yi wannan kira ne a lokacin da take amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan kammala taron Majalisar Zartarwa.
Hajiya Ramatu Aliyu wacce ta shawarci gwamnati mai jiran gado da kada tayi nadin irin wannan mukami ga mambobin majalisar ministocin ta, ta ce manyan ministoci suna shafe karfin ikon kananan ministoci.