On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Babu Tanadin Aikin Kidiyar 'Yan Najeriya A Cikin Kasafin Kudin 2024 - Majalissa

Alamu na nuni da cewa babu wani tanadi da aka tsara na kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2024 a cikin kudirin kasafin kudin 2024 na hukumar kidaya ta kasa.

Mambobin kwamitin majalisar dattijai kan kasafin kudi sun kadu a ranar Talata lokacin da aka sanar da halin da ake ciki.

Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan kidaya, Sanata Abdul Ningi, ya sanar da ‘yan majalisar game da al'amarin a lokacin da yake gabatar da rahoton kasafin kudin hukumar kidaya na shekarar 2024 ga kwamitin tattara bayanai.

Ya shaida wa kwamitin cewa idan ba a samar da kudin kidayar a cikin kasafin kudin kasa ba, kasar nan za ta yi asarar kusan Naira billiyan 200 da hukumar kidaya ta kasa ta kashe wajen aikin kawo yanzu.

Sai dai ya bayyanawa kwamitin cewa hukumar za ta bayyana yau Laraba tare da bayanan nawa suke bukata don gudanar da kidayar jama’a a shekarar 2024.