Hukumar Zabe ta kasa Mai zaman Kanta, Ta fitar da Jadawalin Sunayen Mutanen da zasu yi takara akan wasu mukamai daban-daban a yayin babban zaben kasar nan na Badi.
To sai dai a cikin jadawalin da Hukumar ta fitar, Ba’a ga sunan Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan da kuma Tsohon Ministan Raya Yankin Naija Delta Godswil Akpabio da kuma na gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ba.
Mutanen ukku dai sun shiga zaben fidda gwani na shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, To sai dai kuma daga biya sunyi mi’ara koma baya akan takarar kujerar sanata, bayan kayen da suka sha a zaben fidda gwani na shugaban kasa.
A wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na kasa a daren jiya, Kwamishinan Hukumar zabe, Kuma shugaban kwamitin Yada Labaranta, festus Okoye, Yace ba za’a tursasawa hukumar wallafa sunayen Yan takarar da basu shiga zaben fidda gwani na jam’iyyunsu ba.