Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi gargadi ga masu rike da sarautun gargajiya a jihar da su kaucewa siyasar bangaranci, yana mai cewa irin hakan zai zama sabawa tsarin gargajiya.
Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a jawabinsa na karshen mako, jim kadan bayan mika sandar mulki ga mai martaba Sarkin Katagum na 12 da ke karamar hukumar Katagum, Alhaji Umar Faruk na II.
Gwamna Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta amince da irin wannan hali ba, yana mai nuni da cewa duk da cewa su na kowa ne amma bai kamata su karkata a wani bangare ba.
Mohammed ya kuma yi gargadin cewa sakamakon rahotannin da ya samu na wasu sarakunan gargajiya a jihar da ake zargin suna da hannu a salwantar da wuraren kiwo da dazuzzuka da burtalai a jihar, ba zai bar duk wanda aka samu da laifi ba.