Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta kammala bincike na farko kan Fatima Malam, wadda ake zargin ta dabawa Sharifah Usman ‘yar shekara 8 wuka.
Da yake zantawa da wakiliyarmu Amina Garba, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce kowanne lokaci daga yanzu za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban Kotu.
A cewarsa, bayan kammala binciken tuni rundunar ‘yan sanda ta mika takardar karar zuwa ma’aikatar shari’a domin daukar mataki na gaba.
Ya kara da cewa bincike ya tabbatar da cewa wacce ake zargin tana da hankali da kuma lafiyar kwakwalwa, wanda hakan ya karyata labarin rashin lafiyar da mijin nata ya bayar.
Idan za’a iya tunawa dai an kama Fatima ne a ranar 18 ga watan Mayu a maboyarta achan jihar Jigawa, bayan ta yi yunkurin kashe ‘yar makwabtanta mai shekaru 8 saboda zargin mahaifinta ya shawarci mijinta ya kara Aure…