A yanzu haka dai a iya cewa ta leko ta koma, kan maganar yuyuwar yin Hadaka tsakanin Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da kuma Dan Takarar shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda rahotanni suka tabbatar da cewa a halin yanzu babu wannan maganar.
Kusa a jam’iyyar LP, Doyin Okupe ya baiyana cewa babu wani shiri na yin Hadaka a tsakanin jam’iyyun biyu kamar yadda wasu da dama ke tsammani.
A wata hira da aka yi da Sanata Kwankwaso a kwanan nan, Yace tabbas da hadakar zata yuyuwa shine abunda akafi so, to amma ba zai yadda ya zama mataimakin Peter Obi ba.
Kazalika rahotanni sun tabbatar da cewa dukkanin mutanen biyu babu wanda yake son ya zama Dan Takarar Mataimakin shugaban kasa, A yayin da Doyin Okupe yace tuni aka binne maganar yuyuwar yin Hadaka a tsakaninsu.