Babban jojin Najeriya mai shari;a Olukayode Ariwoola ya ce babu wata suka duk zafinta ko wani ra’ayin jama’a da zai sa bangaren shari’a ya yi wasu abubuwa da suka ci karo da kundin tsarin mulkin kasa, a shari’oin dake gaban kotunan kasar nan.
Alkalin Alkalan na kasa ya ce wajibi ne Alkalai su yi aiki da doka a lokacin da suke yanke hukunci akan kowacce irin shari’a.
Mai shari’a Ariwoola ya baiyana haka ne a ranar Laraba lokacin da yake rantsqar da sabbin alkalan babbar kotun tarayya guda 23, wanda daga cikinsu hadda dansa mai suna Olukayode Ariwoola.
Ya kuma yi gargadin cewar ba za’a saurarawa duk wani alkali da aka samu da yin ba daidai ba a lokacin zaman shari’a.
Y ace hukumar shari’a ta kasa zata dauki mataki mai tsauri akan Alkalan da aka samu da sakaci wajen gabatar da aikinsu.