Gwamnatin tarayya ta umarci babban bankin kasa CBN ya gudanar da taro duk wata uku da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje da ke aiki a Najeriya a wani mataki na biyan kudaden da suke bi bashi.
Ministan sufurin jiragen sama da kula da sararin samaniya, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja, yayin taron sufurin jiragen sama karo na 7.
Kafin wannan umarni da ministan ya bayar, kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suna shan wuya wajen samu kudadensu saboda manufofi da tsare-tsaren Najeriya na musayar kudaden waje.
Keyamo ya ce ya yi amanna cewa dole ne a bi hanyar da ta dace wajen samun mafita mai dorewa kan batutuwan.