Babban bankin kasa CBN ya gargadi masu cin zarafin Naira da su daina, ko kuma su fuskanci dauri a gidan gyaran hali.
Ta yi gargadin cewa har yanzu dokar da ta haramta watsa takardun naira da sunan yin li’ki, musamman a wuraren taruwar jama’a nan daram
Babban bankin kasar, Ya ce Wadanda suke aikata laifin zasu iya fuskantar daurin wata shida a gidan gyaran hali ko kuma tarar naira dubu 50
Shugabar, Sashen Ayyuka ta bankin, Ngozi Etim, ita ce tayi wannan gargadi.
Ta ce CBN na aiki tare da jami’an ‘yan sanda da na hukumar EFCC da kuma hukumar kula da harkokin mu’ammalar kudi ta kasa domin dakile cin zarafin naira da ake yi.