
Babban bankin kasa ya musanta wasu rahotanni dake baiyana cewar yana duba yiyuwar janye sabbin takardun naira ‘yan 200 da 500 da kuma dubu 1 da aka sauyawa fasali daga cigaba da zagayawa a hannun jama’a.
Wata sanarwa da kakakin bankin, Isa Abdulmumin ya fitar a ranar Lahadi, Ya baiyana rahotannin a matsayin na shakulatin ‘bangaro da basu da tushe balle makama.
Sanarwar ta baiyana cewar sabbin takardun kudin zasu cigaba da yin aiki har nan da ranar 31 ga watan Disambar Bana, Lokacin da za’a dena amfani da tsaffin takardun kudin.