Babban Bankin kasa ya ce kawo yanzu ya karbi jimillar tsaffin kudi har naira bilyan 165, tun bayan kiran da ya yiwa jama’ar kasar nan, kan su mayar da tsaffin kudin nasu bankunan ajiya.
Daraktan harkokin kudi na Babban bankin Kasa, Rasheed Adams ne ya baiyana haka a yayin taron kwamitin tsara manufofin kudi na kasa yau a Abuja.
Yace wata daya bayan sanarwar da aka yi, Yawan adadin tsaffin kudin da bankin ya karba sun zarta wanda yayi tsammanin zai karba zuwa yanzu.
Sai dai kuma ya baiyana takaicinsa kan yadda wasu tsirarun yan Najeriya ke neman kara wa’adin mayar da tsaffin kudin na Naira, yana mai cewa wa’adin da bankin ya bayar na ranar 23 ga watan janairun sabuwar shekara na nan daram.