Babban bankin kasa CBN, Ya ce tsaffin takardun kudi na naira da aka sauyawa fasali zasu cigaba da yin aiki har sai abunda hali ya yi.
Idan ba’a manta ba, A cikin watan Octoban bara ne, Babban bankin kasar ya bullo da sabbin takardun kudi yan naira 200 da 500 da kuma naira dubu 1, Sannan kuma ya saka wani wa’adi da za’a dena amfani da tsaffin takardun kudin a wancan lokaci.
To sai dai a sanarwar da Babban bankin kasar ya fitar a ranar Talata, Ya ce yana sanar da al’umma cewar ya tsawaita wa’adin cigaba da amfani da tsaffin takardun kudi yan naira 200 da 500 da kuma dubu 1 har sai abunda hali ya yi.
Sanarwar wadda ta fito ta hannun kakakin babban bankin Isa Abdulmumin, Ya ce rassan babban bankin kasa zasu cigaba da karbar tsaffi da kuma sabbin takardun kudi daga hannun bankunan ajiya.
Haka zalika bankin ya ce yana aiki tare da hukumomin da abun ya shafa domin ganin an janye hukuncin da kotu ta yanke kan amfani da sabbin takardun kudin nan bada jimawa ba.