Babban bankin kasa CBN, Ya ce babu wani karin wa’adin yin amfani da tsaffin takardun kudi na naira da aka sauyawa fasali da zai yi a nan gaba.
Yan Najeriya cikinsu hadda gwamnoni sun bukaci babban bankin kasar ya tsawaita wa’adin yin amfani da tsaffin kudin a saboda karancin sabbi da ake fama dashi yanzu haka.
To sai dai kuma, Gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele , Ya ce babu wani karin lokaci na yin amfani da tsaffin kudin da bankin zai yi,bayan karewar kwanakin goman da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dasu.
Gwamnan ya baiyana haka ne a birnin Ikko, yayin wani taron manema labarai da aka yi dashi a jiya, Inda ya roki jama’ar kasa dasu kara yin hakuri, tare da baiyana cewar ribar da za’a samu game da tsarin zai fi kalubalen da ake fuskanta.