Daga karshe dai babban bankin kasa ya magantu kan hukuncin da kotun koli na bada umarnin cigaba da amfani da tsohon Kudi.
Babban bankin Kasa ya amince da cigaba da yin amfani da tsaffin takardun kudi na 200 da 500 da kuma naira Dubu 1.
A daren jiya ne babban bankin kasar ya tabbatar da amincewarsa na cigaba da amfani da tsaffin takardun kudin. Wannan mataki na zuwa ne bayan shafe tsawon kwanaki Goma da hukuncin da kotun koli ta yanke, na bada umarnin cigaba da amfani da tsaffin takardun kudin.
Sanarwar da Kakakin Babban bankin kasa, Isa Abdulmumin ya fitar, Ta baiyana cewar Babban bankin ya umarci sauran bankuna dasu fara bayarwa da kuma karbar tsaffin takardun kudi.
Kazalika babban bankin kasar ya baiyana cewar ya gana da kwamitinsa mai kula da harkokin bankuna,inda bada umarnin cigaba da amfani da tsaffin takardun kudin har nan da ranar 31 ga watan Disambar bana.
A saboda haka babban bankin kasar ya umarci dukkanin wadanda abun ya shafa dasu fara aiki da wannan umarni a nan take.