On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Ba Za'a Sake Fuskantar Karin Farashin Man Fetur Ba - Fadar Shugaban Najeriya

Gwamnatin tarayya  ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewar ba za a kara farashin man fetur a fadin kasar ba.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan ga manema labarai na  fadar shugaban kasa.

Bugu da kari  yaga baiken  barazanar da kungiyar kwadago ke yi na shiga yajin aikin gama gari sakamakon karin farashin da ake yayatawa, ba tare da bincike ko tabbatar da gaskiyar lamarin ba.

Ya ci gaba da cewar manufofin gwamnati na daidaita yanayin tafiyar da albarkatun man fetir  karkashin shugaban kasa  Bola  Tinubu ba za’a bari su cutar da talakawa  ba.