Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makarantun Sakandire Ta Kasa, NECO, Ta baiyana cewa bata tsara cewar za’a rubuta jarabawa a ranar 9 ga watan da muke ciki ba, Sabanin wasu rahotanni dake baiyana cewa Hukumar ta saka jarabawa da za’a a yi a ranar Idin Babban Sallah.
Hukumar ta baiyana haka ne ta cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun shugaban sashin yada labaranta da kuma Hulda da Jama’a, Abdul’aziz Sani wadda aka rabawa manema labarai yau a Abuja.
Ya kara da cewa Hukumar tana sane da irin muhimmancin bukukuwan da suka shafi addini suke dashi, wanda hakan yasa take yin tanadi na musamman wajen saka ranar da za’a gudanar da jarabawa a irin wannan lokaci.
Idan za’a iya tunawa an fara jarabawar Kammala Manyan Makarantun Sakandire ta kasa a ranar 27 ga watan jiya, Sannan kuma za’a kammala ta a ranar 12 ga watan Augustan bana.