On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ba Za’a Lamunci Cin Zarafin ‘Yan Sanda A Najeriya Ba – Alkali Baba

Babban Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasarnan Usman Alkali Baba, ya yi gargadi kan karuwar hare-haren da ake kaiwa jami’an ‘yan sanda sanye da kayan aiki a wurare daban-daban a fadin kasar nan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a a Abuja, ya kuma yi Allah wadai da yadda ake cin zarafin jami’an ‘yan sanda sanye da kakinsu lokacin da suke  gudanar da ayyukan rundunar da doka ta dora musu.

“Sufeta Janar ya yi gargadin cewa, daga yanzu, rundunar ‘yan sandan ba za ta lamunci  duk wani hari da aka kai akan jami’anta ba, saboda muna daukar rayukansu da matukar muhimmanci.

“A dalilin haka, babban Sufeta Janar, ya bai wa dukkan rundunonin kasar umarnin cewa, daga yanzu, duk wanda aka kama da laifin kai hari kan wani jami’in tsaro, a tabbata a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.” Acewar Sanarwar.