Sanarwar ta kara da cewa bayan Farfesa Ango ya kammala aikin...
Shugabannin Kungiyar Dattawan Arewa sun nesanta kansu da matsayar da wasu daga cikinsu suka dauka na mara wa Sanata Bukola Saraki da Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed baya amatsayin 'yan takarar da yankin arewa ya amince su tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.
Cikin wata sanarwa da babban jami'in yada labarai na kungiyar Dr Hakee Baba-Ahmed ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce ba a shigar da kungiyar a cikin hanyoyin da aka bi na yanke wannan shawarar ba.
Yace, "Ya zama dole mu mayar da martani kan labarin da ke yawo da ke nuna cewa Kungiyar Dattawan Arewa ta taka rawa wajen fitar da wasu 'yan takara cikin manyan 'yan takarar jam'iyyar PDP ta hanyar sasantawa tsakaninsu,"
Sanarwar ta ce "'Yan takarar ne da kansu suka yi wannan yunkuri. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Gwamna Bala Mohammed da Bukola Saraki da kuma Malam Mohammed Hayatudeen sun sanar tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida aniyarsu, kuma sun bukaci ya shiga cikin maganar a matsayinsa na dattijo."
Sanarwar ta kuma ce, "Janar Babangida ya bukaci shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ya tsara wata hanya da za a bi wajen yin maslaha tsakanin 'yan takarar hudu."
Sai dai ba a matsayinsa na daya daga cikin jagororin Kungiyar Dattawan Arewa ya yi wannan aikin ba - ya yi shi ne a matsayinsa na Farfesa Ango Abdullahi, in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa bayan Farfesa Ango ya kammala aikin, ya fitar da wani cikakken bayani da shawarwari, kuma ya sanya wa rahoton hannu a matsayinsa na Ango Abdullahi, saboda haka ne Kungiyar Dattawan Arewan ta ce ba da ita aka yi aikin ba:
"Kungiyar Dattawan Arewa ba ta da alaka kai tsaye da wata jam'iyyar siyasa ko wani dan takara, kuma ta mayar da hankali ne wajen samar da shugabanni na gari a zabukan shekarar 2023. sannan ta yi imani cewa akwai nagartattun 'yan takara da ya dace a bar wa jam'iyun siyasar kasar nan su zabo da kansu."