Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da Abdu Maikaba a matsayin sabon mai horas da tawagar sai masu gida ta kano Pillars,inda ta kulla kwantiragin shekaru biyu da shi.
Audu Maikaba zai samu temakon Abubakar Abubakar wanda aka fi sani da Senior sai Ahmed Garba Yaro-ro da Gambo Muhammad da kuma Auwalu Abbas a matsayin mai horas da mai tsaron raga na kungiyar.
A yayin kwarya-kwaryar bukin kaddamar da sabon mai horaswar, Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdul Salam ya bukace da ya zage damtse wajen ganin ya farfado da martabar kungiyar.
Ya kuma baiyana cewar gwamnatin kano a shirye take ta bada duk wani goyon bayanta wajen cigaban kungiyar , tare da bada tabbacin cewar nan bada jimawa ba gwamnati zata gyara filin wasa na Sani Abacha dake Kofar mata.
Shima shugaban kungiyar, Alhaji Babangida Umar Litle yace nadin da aka yiwa Abdullahi Maikaba anyi shine bisa cancanta kuma suna da kwarin gwiwar cewar zai farfado da kungiyar.