Dan Takarar shugabancin Najeriya karkashin Jam'iyyar PDP a zaben badi Atiku Abubakar ya sake jaddada aniyar sa ta tabbatar da hadin kan kasar nan, inda yace ita ce hanya mafi sahihanci wajen samar da cigaban da ake bukata.
Atiku ya sami gagarumar tarba cikin kasaitaccen biki a garin na Jada, inda ya samu rakiyar manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP na ciki da wajen jihar.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasar kan al'amuran da suka shafi yada labarai, Abdulrasheed Shehu, wadda aka rarraba ta ga manema labarai a fadin kasar nan.
Da yake masa maraba, cikin kasaitaccen yanayi da aka shirya na musamman, shugaban karamar hukumar Jada honorable Salisu Muhammed Solo yace suna mutukar alfahari da kasancewar Atiku dansu, inda ya yi alkawarin mara masa baya a Takarar shugabancin Najeriya da yake yi
A jawabin sa yayin taron, Sanata Dino Melaye ya bayyana muhimmancin ziyayar zuwa gida, inda yace wannan ya nuna cewar Atiku ya san asalin sa ba kamar wasu yan takarar ba wadanda suke cike da rudani game da asalinsu.Yace Atiku shi ne Dan Takarar daya fi cancanta kasancewar sa ba Mai kabilanci ba Wanda ya ke da dukkan abinda ake Bukata domin ceto Najeriya Daga mummunan yanayin da take ciki.
Gwamnan jihar ta Adamawa Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri godewa Atiku ya yi saboda shigowa cikin al’umar sa. Inda ya bawa Dan Takarar ta PDP tabbacin cewar zasu Yi aiki domin nasarar sa a zaben, domin bashi damar amfani da kwarewar sa da kishin sa wajen ceto Najeriya.
Da yake mayar da jawabi, Dan Takarar shugabancin Najeriya na Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya godewa mutanen nasa saboda Addu'o'in su da fatan alheri. Ya kuma Yi kira gare su da su sauke nauyin dake kan su na yin zabe domin bashi damar karbar kasar don inganta makomar kowa. Inda ya jaddada aniyar sa ta kasancewa Jakada na gari ga mutanen sa da kasar Baki Daya inda ya yi alkawarin aiki domin dawo da zaman lafiya da haÉ—in Kai da ci gaban kasa idan aka zabe shi.