Dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, Ya sake nanata kudirinsa na tabbatar da an samu cigaba ta bangaren shigar da matasa cikin harkokin siyasa da kuma jagoranci.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin Hadiminsa na musamman ta bangaren yada Labarai, Abdurasheed Uba Sharada, a yayin wata hira ta musamman da aka yi dashi ta wayar salula, Inda ya bada tabbacin kaso 40 bisa 100 na nade-naden da za’a yi a gwamnatinsa zasu tafi ne wajen matasa.
Kakakin Dan takarar shugaban kasar mai shekara 33 a duniya, wanda a kwanan nan ne aka yi masa nadin, Ya fadawa wakilinmu Abdurrahman Balarabe Isah cewa, Maigidan nasa ya himmatu wajen ganin matasa masu kishi da fikira sun kasance jagororin kasar nan a nan gaba kadan.
Bugu da kari ya baiyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a kowane lokaci yana yin tafiya ne tare da jajirtattun matasa yan kasa ta bangaren kasuwanci da kuma Siyasa.