A ranar Talata ne Dattawan Jam’iyyar PDP dake zauren majalisar dattawa ta kasa suka gana da Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da kuma Mataimakinsa Gwamna Ifeanyi Okowa.
Taron wani bangare ne na kokarin sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar da suka harzuka gabanin babban zaben kasar nan dake tafe.
Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka hada da gwamna Nyesom Wike na daga cikin wadanda suka nuna rashin jin dadinsu game da yadda harkokin jam’iyyar ke kasancewa.
To sai dai kuma Atiku Abubakar Yaci alwashin sake hada kan yayan jam’iyyar wuri daya gabanin zabe mai zuwa. Daga cikin wadanda suka halarci ganawar hadda shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu.