Kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, Tace har yanzu tana dakon jin amsar da gwamnatin taraiyya zata bata game da bukatun data gabatar mata, domin duba yuwar ko zata janye yajin aikin data shafe watanni 4 tana yi.
Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Emmanuel Osodoke ne ya baiyana haka yayin ganawarsa da manema Labarai a ranar Lititin, Yace janye yajin aikin ya ta’allaka ne da yadda gwamnatin taraiyya ta dauki mataki akan bukatun kungiyar da aka gabatarwa kwamitin da gwamnatin taraiyya ta kafa, a karkashin farfesa Nimi Briggs.
Ya kara da cewa gwamnati tayi alkawarin cewa zata dauki matakan da suka dace cikin gaggawa, wanda hakan yasa itama kungiyar ta kwantar da kanta domin ganin abunda zai faru.
Sai dai a lokacin da aka tuntubi shugaban kwamitin Farfesa Briggs domin jin ko sun sake ganawa da kungiyar ASUU, Ya baiyana cewa kwamitin bashi da hurumin daukar mataki na karshe akan abubuwan da suka tattauna sai dai gwamnati.