Shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya caccaki ministan kwadago da nagartar aiki, Chris Ngige, bisa zarginsa da ba da izinin biyan rabin albashin watan October ga malaman jami’oi.
Hakan na zuwa ne bayan ASUU a watan Oktoba ta dakatar da yajin aikin data shafe tsawon watanni 8 tana yi bisa ga umarnin da kotun ma’aikata ta kasa ta bayar, na cewar malaman su koma bakin aiki.
Osodeke ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin wata hira da aka yi dashi ta cikin shirin Siyasa a yau na gidan talabijin na Channels, inda ya jaddada cewa, kasancewar Ngige ya garzaya kotu, ya rasa ‘yancin da yake dashi a matsayinsa na mai shiga tsakani, kuma bashi da wani bakin magana akan abunda ke tsakanin kungiyar da gwamnatin taraiyya.
Shugaban kungiyar ASUU na kasa ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a warware matsalolin da kungiyar ke ciki, domin amfanin dalibai da iyaye dama kasa baki daya.
Idan za’a iya tunawa, wasu rassan kungiyar malaman jami’oi ta ASUU kamar UNILAG dake Legas da Abuja, sun gudanar da zanga-zangar yin daya dangane da biyansu rabin albashi, A yayin da itama jami’ar Bayero dake nan Kano zata nuna nata boren a ranar Alhamis mai zuwa.