Jami’oin kasar nan na fama da matsalar karancin Ma’aikata, a yayin da dubban malaman manyan makarantun ke haurawa zuwa kasashen waje domin samun aiki mai gwabi, daidai lokacin da masu yin ritaya a jami’oin ke karuwa.
Da dama daga cikin rassan kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU sun tabbatar da haka ga jaridar Punch, inda suka alakanta matsalar, da yadda malaman jami’oin ke tafiya kasashen waje domin samun aiki, da kuma matsalolin da suka dabaibaye tsarin biyan albashi na bai daya ga malaman jami’oi mai taken IPPIS.
A jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, Kimanin malaman 100 ne suka bar jami’ar, ayayin da jami’ar gwamnatin tarayya ta Gusau dake zamfara ke bukatar samun malamai kimanin dubu 1 domin cike guraben darussan da babu malaman dake koyar das u.
Haka zalika kungiyar ASUU t ace a jami’ar koyar da aikin gona ta Abeokuta dake Ogun, sama da gurabe 350 na malamai ne babu kowa akansu, a yayin da malamai 27 suka bar tsangayoyi daban daban na jami’ar Legas, sai kuma Malamai guda 100 da suka bar aikin a jami’ar Uyo, inda suka fice zuwa kasashen waje.
To wannan matsala dai na zuwa ne a yayin da yanzu haka akwai kimanin kudurorin doka har guda 32, dake gaban zauren majalisar wakilai da kuma ta Dattawa, dake neman kafa sabbin jami’oi da kwalejojin fasaha da kuma kwalejojin ilimi, tun bayan rantsar da sabon zauren majalisar na 10 da aka yi a bana.
A yanzu haka akwai jami’oin gwamnatin tarayya guda 52 sai jami’oin jihohi guda 63 da jami’oi masu zaman kansu guda 147, sai kwalejojin kimiyya da fasaha na gwamnatin tarayya guda 40, da kuma na jihohi guda 49, sai kwalejojin fasaha masu zaman kansu guda 76 da kuma kwalejojin ilimi har guda 219.
Rahotanni sun baiyana cewar kakakin majalisar wakilai na cigaba da matsa lamba domin ganin a gina sabuwar Jami’ar kimiyya ta gwamnatin tarayyya a jihar Kaduna.
Sai dai kungiyar ASUU da kuma sauran kwararru a bangaren ilimi sun gargadi gwamnati kan kafa wasu sabbin jami’oin a yayin da ta kasa rike wadanda ake da su a halin yanzu.