Kungiyar Malaman Makarantun Fasaha a Najeriya ASUP tayi kira ga gwamnonin jihohin Abia da Osun da Plateau da Benue da Edo da Ondo da Ogun da kuma Sokoto da su biya albashin mambobinta kafin su kammala wa’adinsu a ranar 29 ga Mayu na 2023.
Da yake zantawa da manema labarai a karshen taron kungiyar a ranar Alhamis, Shugaban ASUP, Anderson Ezeibe ya zargi gwamnonin da rashin nuna dattako tare da jefa malaman cikin wani hali a jihohinsu.
Ezeibe ya kuma yi kira ga ma’aikatar ilimi da ta mutunta hukuncin da kotun ma’aikata ta kasa ta yanke, ta hanyar sallamar shugabannin makarantun gwamnatin tarayya na Ugep da Shendam da Mungonu da Wannnune, da kuma Ohodo daga matsayin shugabanni na kwalejojin.