'Yar wasar gaba ta kungiyar kwallon kafaer Mata ta kasa Super Falcons Asisat Oshoala ta lashe kyautar gwarzuwar Yar wasa ta Afirka karo na biyar.
Oshoala, wadda ke buga wasanta a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ta doke Grace Chanda daga kasar Zambia da Ajara Nchout Njoya daka kasar Cameroon wadda ke bugawa kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan wajen lashe kyautar.
Nasarar data samu, tasa ta zarce 'yar wasa Perpetual Nkwocha a matsayin 'yar wasan da ta fi lashe kyautar gwarzuwar yar wasa ta nahiyar Afirka.
Oshoala mai shekaru 27, It ace Yar Najeriya daya tilo da aka zaba domin shiga cikin jerin sunayen karshe da aka tantance domin samun wanda zai lashe kyautar a shekarar 2022.