Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Zai fara Dashen Bargo wanda hakan zai sa ya zama na biyu cikine jerin asibitocin koyarwa dake kasar nan, da suke yin irin wanan aikin.
Shugaban Asibitin Farfesa Abdulraham Abba Sheshe ne ya baiyana haka yayin kaddamar da sashin kula da cututtukan da suka shafi jinni, wanda wani dan asalin jihar Kano, Injiniya Umar Ibrahim ya samar.
Ta cikin wata sanarwa da Daraktar Hulda da jama’a ta Asibitin Hauwa Mohammed Abdullahi ta fitar, Ta baiyana cewa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas ne kadai ke yin Dashen Bargo a kasar nan.
Hoton Bargo
Daga nan sai ya godewa Injiniya Umar sanan kuma yayi masa addu’ar samun tukwici da gidan Aljanna.