A yau ne za a fara buga wasannin zagaye na 32 na gasar cin kofin tarayya na shekarar 2023 tare da tsaffin wadanda suka lashe gasar Rangers International FC dake Enugu da Kano Pillars yau a Abuja. A baya Kano Pillars ta taba haduwa da Ranges sau 14, inda ta yi nasara a wasanni biyar, ta yi kunnen doki biyar
A wani bangaren kuma, Martin Odegaard ya temakawa kungiyar ta Arsenal zuwa saman teburin gasar Premier yayin da dan wasan tsakiya na kasar Norway ya zura kwallaye biyu a ragar Chelsea a wasan da aka tashi da ci 3 da 1 a ranar Talata.
A karshe kuma kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain ta dakatar da Jagoran tawagar yan wasan Argentina Lionel Messi na tsawon makwanni biyu bayan ya tafi kasar Saudiyya ba tare da izinin kungiyar ba a wannan makon.