Arsenal ta kammala cinikin fan miliyan 65 domin sayen dan wasan Jamus Kai Havertz daga kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake Landan kan kwantiragi na dogon lokaci kamar yadda tya tabbatar da matakin a shafinta na internet a jiya.
Havertz ya zama dan wasa na farko da Arsenal ta saya a wannan lokaci, yayin da gunners din kuma ke son kulla yarjejeniya da dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice da dan wasan baya na Ajax Jurrien Timber.
A wani bangaren kuma, dan wasan Senegal Edouard Mendy ya bar Chelsea ya koma kungiyar Al Ahli ta Saudiyya kan kudi fan miliyan 17.
Chelsea ta sanar da komawar Mendy zuwa Al Ahli a shafinta na Twitter ranar Laraba.