shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, Ya amince da cewar ba a tuntubi masu neman mukamai daban-daban a majalisar wakilai ta kasa ba, kafin a cimma matsaya kan yin amfani da tsarin shiyya-shiyya wajen fitar da mukaman.
Adamu ya baiyana haka ne a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja lokacin da wasu masu neman kujerar shugaban majalisar dattawa suka yiwa shalkwatar jam’iyyar tsinke domin nuna fushinsu.
Sanata Abdullahi Adamu ya ce jam’iyyar zata sake yin karatun ta nutsu kan tsarin domin yin abunda ya dace.
Sai dai ya baiyana cewa jam’iyyar ba za ta iya yanke wani hukunci kan lamarin ba, ba tare da tuntubar zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba.