Gwamnan Babban bankin kasa, Godwin Emefiele , Ya ce yawan hada-hadar kudi da aka yi ta hanyar amfani da tsarin nan na eNaira ya kai naira milyan dubu 8 a kasar nan.
Da yake jawabi a Abuja, Gwamna Emefiele , Yace an samu dimbin nasarori tun bayan kaddamar da tsarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar dashi a cikin watan Oktoban 2021.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakiyarsa mai kula da shashin ingancin kudi, Aisha Ahmad, Ta ce tsarin na eNaira yana haifar da Da mai ido.
Kazalika shima da yake nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan babban bankin kasa kula da sashin tsare tsaren tattalin arziki, Kingsly Obiora, Yace ya zuwa wannan lokaci, an sauke manhajar yin hada-hadar kudi ta eNaira har Dubu 927.