A yanzu haka tsohon ministan lantarki, Sale Mamman na a komar shalkwatar hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa dake Abuja, sakamakon zarginsa da almundahanar naira milyan dubu 22. An cafke tsohon ministan ne a ranar Laraba kamar yadda jaridar Daily trust ta baiyana.
Wata majiya ta fadawa jaridar cewar, Sale Mamman wanda ya kasance minister shekarar 2019 zuwa 2021,ana tuhumarsa da hada baki da jami’an ma’ikatar lantarki, tare da karkatar da zunzurutun kudi har naira milyan dubu 22 da aka ware domin aikin samar da tashoshin lantarki na Zungeru da kuma Mambila, inda suka raba kudin a tsakaninsu.
Majiyar ta kuma baiyana cewar an gano tarin kadarori da dukiya a nan gida Najeriya da kuma kasashen waje da ake alakanta su da mallakin tsohon ministan , ya yi da aka samu Milyoyin naira da kuma Dalar Amurika a hanunsa.
Rahotanni sun baiyana cewar tsohon ministan lantarkin zai ci gaba da kasance a hannun hukumar EFCC har zuwa lokacin da zata samun bayanan da take bukata a wajensa.
Har zuwa yanzu dai hukumar ta EFCC bata fitar da sanarwar dakume tsohon ministan lantarkin ba, kawo yanzu da muke baku labarin.