Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da Kakakin Majalisar Jihar Ondo, Bamidele Oleyeloogun, a gaban wata babbar kotu dake birnin Akure bisa zarginsa da almundahanar Naira miliyan 2 dadubu dari 4 a shekarar 2019.
An gurfanar da shi ne tare da wani dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Akoko ta Kudu maso Yamma , Felemu Bankole, da kuma wani ma’aikacin gwamnati a jihar, Segun Bankole, bisa tuhume-tuhume guda biyu da ake masu
Ana tuhumar ‘yan majalisar da yin wadaka da kudaden ne a a lokacin da ya kamata su hudu su halarci wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu da cibiyar samar da ayyukan yi ta kasa da ke Legas ta shirya a ranakun 11 da 12 ga watan Disambar 2019 amma suka karkartar da kudin.
Ana zargin cewar kudaden da ma’aikatar kudi ta jihar ta saki da suka kai Naira miliyan 2 da dubu dari 4 sun shiga aljihun mutanen, Sai dai kuma sun musunta tuhumar da ake masu.
Alkalin kotun, Mai shari’a Adegboyega Adebusoye ya ce ya kamata wadanda ake kara su ci gaba da kasancewa a hannun belin, tare da dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Mayu bana.