Ana zargin Jami’an Hukumar Karbar Korafe korafe da yaki da cin hanci ta jihar Kano da cin zarafin dakataccen shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado, a jiya.
Wadansu mutane biyu daga hukumar sun isa gidan Muhyi dake Sharada cikin wata Mota kirar Honda mai launin ruwan Bula da kimanin karfe 6 da rabi na yammacin jiya, domin kama shi batare da samun umarnin kama shi daga kotu ba, sai dai bisa umarnin da shugaban hukumar Balarabe Mahmud ya basu.
Rahotanni sun baiyana cewa, wani Dan sanda mai matsayin Insifekta, ya yaga rigar Muhyi Magaji a lokacin da yake kokarin tafiya dashi, kafin Makotan Muhyin sufi karfinsa inda kuma daga bisani aka mikashi ofishin ‘yansanda na Sharada.
Muhyi Magaji Rimin Gado ya baiyana al’amarin a matsayin wani yunkuri na yin garkuwa dashi, tare da baiyana cewa jami’an hukumar basu da wata shaida da za’a gane su.
To sai dai a lokacin da aka tuntubi shugaban hukumar Karbar korafe –korafe da yaki da cin hanci ta jihar Kano, Mahmud Balarabe , Ya ce jami’ansa sunje gidan ne domin samun wasu bayanai bawai domin su kama Muhyin ba, inda kuma ya musanta zargin cewar sunci zarafin Muhyin.