Gwamnatin Tarayya ta ce ta dauki nauyin wakilai 422 ne kawai daga cikin ‘yan Najeriya dubu 1 da 411 da aka rawaito suna halartar taron sauyin yanayi na COP28 da ke gudana a Dubai.
Wannan bayanin dai na zuwa ne bayan fusatar da ‘yan Najeriya suka nuna kan yawan tawaga da suka halarci taron, duk da karuwar fatara da yunwa da ake fusknata fadin kasarnan.
Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce an zabo wakilai 422 daga fadar shugaban kasa da majalisar kasa kan sauyin yanayi da dukkan ma’aikatu da ofishin mataimakin shugaban kasa da majalisar dokoki ta kasa, da hukumomin tarayya.
Ya ce, a matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki kuma mafi yawan al’umma a Afirka, da ke da matukar hadari ga sauyin yanayi, Najeriya na da muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufofin taron, don haka shigar da masu ruwa da tsaki babban taron na duniya ya zama dole.