On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Ana Shirin Kaddamar Da Tallafin Kudi Ga Gidaje Milliyan 15 A Najeriya - Beta Edu

Ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci Betta Edu ta ce gwamnatin tarayya za ta kaddamar da shirin  bayar da tallafin kudi ga gidaje miliyan 15 a mako mai zuwa ranar Talata 17 ga watan Oktoba.

Edu ta tabbatar da haka a daren jiya ta cikin wani shirin  gidan talabijin,  watanni bayan gwamnatin tarayya ta dakatar da biyan tallafin man fetur.

Ministar ta ce ana saran samun amincewa daga shugaban kasa kan shirin  a cikin wannan mako da kuma kaddamar da shirin a hukumance a mako mai zuwa.

A cewarta, ma’aikatar tana aiki tare da masu ruwa da tsaki a fadin kasarnan domin samun rijista mai sahihanci ta  wadanda za su amfana domin tabbatar da cewa wadanda ke cikin rijistar ‘yan Najeriya ne da ke samun abunda ya gaza  dala 1.95 a kowacce  rana.