Jihar Kano na alhinin rasuwar Wazirin Kano murabus, kuma Babban limamin Waje, Sheik Mohammad Nasir Mohammad.
Wani daga cikin makusantan iyalansa, Sani Abdallah Wudilawa ya tabbatar da labarin rasuwar marigayin ga Arewa Radiyo.
Babban malamin ya rasu ne a ranar Laraba 7 ga watan Yuni bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya.
Za a gudanar da jana'izarsa yau Alhamis 8 ga watan Yuni a fadar sarkin Kano.
Malamin addinin musuluncin ya rasu yana da shekara 87 a duniya.
A 2014 ne marigayi Ado Bayero ya naɗa Sheikh Nasir sarautar Wazirin Kano naɗin da ya ci karo da turjiya daga gwamnatin jihar Kano ta wancan lokaci.
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, ɗalibansa da al'ummar jihar Kano.
Gwamnan ya bayyana marigayin amatsayin fitaccen malamin addinin Musulunci wanda ya bayar da gudunmawa mai yawa wajen cigaban addinin Musulunci ga daukacin al'ummar musulmin duniya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar, ta ruwaito gwamnan yana kuma bayyana Sheikh Nasir a matsayin wanda ya yi rayuwa abar koyi.