On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Ana Shirin Fara Kai Paspo Har Gida A Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce 'yan Najeriya zasu fara samun Paspo din su har gida ko ofisoshinsu da sauran wuraren da suke so daga shekara mai zuwa.

Ministan harkokin cikin gida O Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Legas yayin da yake jawabi a wajen bikin bude makon jami’ar Legas na 2023.

A cewarsa, nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara morewa tsarin neman fasfo yayin da ma’aikatar ta fara tsara  gudanar da aikin.

Ya ce da wannan mataki ‘yan Najeriya ba za su bukaci su jira sama da makonni biyu kafin su samu fasfo ba.