Daga gobe Talata 4 ga watan da muke ciki na Yuli za'a fara kwaso mahajjatan Najeriya zuwa gida Najeriya.
Shugaban sashin al'amuran jigila na hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON Injiniya Mohammaed Goni Sanda ne ya sanar da haka a birnin Makka.
Sanda ya nunar da cewa da zasu bi tsarin wadanda aka fara kaiwa su za'a fara debowa a yayin jigilar dawo da mahajjatan gida Najeriya.
Injiniya Goni ya kara da cewa kowanne mahajjaci zai san ranar dawo gida ne kawai ta hanyar lissafin kwanaki 40 daga randa ya sauka a saudiyya da karin ko ragin kwanaki 3.
A wani bangaren kuma, Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta ce maniyyatan Najeriya goma sha uku ne suka rasu a aikin hajjin shekarar 2023 a kasar Saudiyya.
Shugaban tawagar likitocin NAHCON, Dakta Usman Galadima ne ya bayyana hakan a birnin Makkah a karhsne mako yayin wani taron tattaunawa bayan Arafa.
Idan dai za a iya tunawa wasu alhazai shida sun rasu a kawanakin baya.
Dr Galadima ya ce mahajjata bakwai sun mutu kafin Misha’ir, yayin da wasu shida kuma suka mutu a lokacin Misha’ir.
Wannan yana nufin alhazai shida sun mutu a cikin kwanaki biyar- hudu a Arafa, biyu a Mina.