Alamu sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya za ta iya fara biyan karin albashin ma’aikatan gwamnati a karshen wannan wata na Afrilu.
Muddin ba’a samu wani sauyi ba, ana saran Shugaba Muhammadu Buhari zai bayar da amincewar sa ta karshe na biyan karin albashi kowanne lokaci daga yanzu.
Kakakin Ma’aikatar Kwadago, Olajide Oshundun ta fadawa jaridar Punch cewa sabon karin albashin da aka yi, zai haifar da karin kashi 40 cikin 100.
Ta ce za a biya basussukan watanni uku na Janairu da Fabrairu da Maris a wani lokaci nan gaba.
Sai dai Oshundun, ta ce ba za ta iya tabbatar da ko shawarar da kwamitin gwamnati wanda ke da alhakin gudanar da aikin ya samu amincewar shugaban kasa ta karshe ba.