A ranar Alhamis ne kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU zata yanke hukunci kan janye yajin aikin data shafe watanni takwas tana yi.
An dai ta yada jita-jita a ranar Litinin dake cewa malaman jami’oin sun janye yajin aikin da suke yi, To sai dai wani daga cikin ‘yan majalisar gudanarwar kungiyar na kasa, wanda ya bukaci a sakaye sunansa, Yace har ya zuwa wannan lokaci ba’a janye yajin aikin ba.
Majiyar ta fadawa manema Labarai cewa , a gobe ne kwamitin kolin kungiyar na kasa zai yi zama na musamman domin daukar matakin da ya dace.
Tun daga ranar 14 ga watan Fabarairun bana ne, Kungiyar ta ASUU ta tsunduma yajin aiki a sakamakon abunda ta baiyana na gazawar gwamnati wajen biya mata bukatunta.