Wasu rahotanni na baiyana cewar takarar da tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ke yi na zama shugaban majalisar dattawa ta gamu da cikas, yayin da wata majiya ta baiyana cewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye goyon bayan da yake yi masa.
Idan ba a manta ba jam’iyyar (APC) ta bayyana amincewarta da Sanata Godswill Akpabio da wasu mutane uku a matsayin jagororin majalisar dokokin ta kasa.
Sai dai matakin bai yi wa wasu ‘ya’yan jam’iyyar dadi ba, musamman masu neman kujerar shugabancin majalisar dattawa da ta wakilai, biyo bayan fushinsu da suka nuna kan daukar matakin.
Rahotanni sun baiyana cewar Sanatoci musamman ‘yan yankin Kudu maso Yammacin kasar nan , zasu yi wata ganawa a tsakaninsu gobe, domin baiyana matsayar su kan matakin.